1 Nuwamba 2026 - 22:04
Source: ABNA24
Tanzaniya: An Sanya Rawuna Ga Ɗaliban Da Suka Kammala Karatu A Hauza Ta Al-Qa'im (A.S) + Hotuna

Wannan biki wani ɓangare ne na ƙoƙarin ƙarfafa tarbiyyar malamai da masu hidimar addini waɗanda ke da ikon gudanar da ayyukansu na ilimi, tarbiyya da zamantakewa bisa koyarwar Alkur'ani Mai Girma da Ahlul-Bayt (A.S)

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Bayt (AS) – ABNA – ya ruwaito cewa: An gudanar da taron bikin sanya rawuna tare da wa'azin tunatarwa daga Sheikh Hemed Jalala ga waɗanda suka kammala karatun kan nauyin da ya rataya a wuyansu na hidimar addini, ilmantar da al'umma da kiyaye ɗabi'u da al’adun musulunci bayan kammala karatunsu na Hauza.

Maulana Sheikh Hemed Jalala, babban Sheikh na Ƙungiyar Shi'a Ithna Ashari ta Tanzaniya (T.I.C) a cikin ziyarsa ta wa'azi, ya sanya rawuna ga ɗaliban da suka kammala karatunsu na addini bayan kammala karatun shekaru biyar a Hauza ta Al-Qa'im (A.S), da ke birnin Tanga, a ƙasar Tanzaniya.

An gudanar da wannan biki ne tare da wani ɗan gajeren jawabi da Maulana Sheikh Hemed Jalala yayi, inda ya yiwa waɗanda suka kammala karatun wa'azi da muhimman umarni kan nauyin da ke gabansu bayan kammala karatunsu na Hauza.

Wannan biki wani ɓangare ne na ƙoƙarin ƙarfafa tarbiyyar malamai da masu hidimar addini waɗanda ke da ikon gudanar da ayyukansu na ilimi, tarbiyya da zamantakewa bisa koyarwar Alkur'ani Mai Girma da Ahlul-Bayt (A.S).

……………..

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha